Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha

Amurka ta yi barazanar karya yarjejeniyar nukiliya

Amurka ta yi barazanar janyewa daga yarjejeniyar takaita mallakar makaman nukiliya muddin Rasha ta ci gaba da karya dokokin yarjejeniyar.

A can baya Rasha ta musanta wanzuwar makaman masu linzami samfurin 9M729
A can baya Rasha ta musanta wanzuwar makaman masu linzami samfurin 9M729 REUTERS/Yonhap
Talla

Kimanin shekaru biyu kenan da Amurka ke korafin cewa, Rasha ta sa kafa ta shure dokokin yarjejeniyar ta shekarar 1987 musamman ganin yadda ta tanadi wasu makamai masu linzami da ake harbawa daga doran kasa.

Wakilin Amurka ta fannin kwance damarar makamai, Robert Wood ya shaida wa manema labarai a birnin Geneva cewa, ba za su lamunnce wa Rasha ba, kuma dole su dauki matakan warware matsalar keta yarjejeniyar mai matukar muhimmanci.

Wood ya ce, batun matsawa Rasha lamba don ganin ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar, shi ne zai fi daukan hankali a wani taro da za su gudanar a makon gobe a zauren Majalisar Dinkin Duniya a New York.

Sai dai Rashan ta sha fadin cewa, ko kadan makaman nata masu linzami samfurin 9M729, ba su karya dokokin yarjejeniyar ba, yayin da a gefe guda Amurkar ke cewa, ai a can baya ma, Rashan ta musanta wanzuwar wadannan makamai.

Su ma shugannin Kungiyar Tsaro ta NATO sun nuna damuwa kan makaman na 9M729, in da suka bukaci Rasha da ta shiga tattauanawar kare makomar wannan yarjejeniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.