Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya-Yemen

A yau' ake buda taron sulhunta yakin kasar Yemen a Geneva

A yau alhamis ake fara taron sulhunta bangarori masu hamayya da juna a rikicin kasar Yemen, taron da MDD ke daukar nauyin gudanarwa a birnin Geneva.Da farko dai tawagar mayakan ‘yan tawayen kungiyar Huthi ta yi ikirarin cewa, ba sa cikin yanayin barin kasar ta Yemen domin halartar wannan taro, to sai dai manzon musamman na MDD dangane rikicin Martin Griffiths, ya ce, sun dauki dukanin matakan da suka wajaba don tabbatar da cewa, bangarorin da ke rikicin sun halarci taron na yau.

wani Sojin Yemen na buda wuta a kudancin filin jirgin saman  Hodeida 15 yuni 2018.
wani Sojin Yemen na buda wuta a kudancin filin jirgin saman Hodeida 15 yuni 2018. AFP
Talla

Dukkanin bangarorin, sun fahinci cewa lokaci ya yi da ya kamata su zauna domin samar da mafita dangane da wannan rikici da ya yi sanadiyar mutuwar mutane masu tarin yawa.

Lura da irin illolin da wannan rikici ya haddasa ne, muka gayyaci dukkanin bangarorin zuwa taron birnin Geneva, mun aika wa gwamnatin Yemen da sauran kungiyoyin da ke dauke da makamai goron gayyata.

Kowanne daga cikinsu kuma, ya tabbatar da cewa a shirya yake ya aiko da tawagar da za ta wakilce shi, yayin da a namu bangare muka dauki dukkanin matakan da suka wajaba domin sauwaka masu damar isa zauren taron, a cewar Mr Martin Griffiths

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.