Isa ga babban shafi
Amurka

Makusantan Trump na fuskantar barazanar dauri a gidan yari

Wasu mahukunta biyu ga shugaban Amurka Donald Trump na fuskantar hukuncin dauri a gidan yari, bayan da kotunan suka same su da aikata laifufuka.

tsohon lauyan Donlad Trump Michael Cohen,  21/08/2018
tsohon lauyan Donlad Trump Michael Cohen, 21/08/2018 REUTERS
Talla

Na farko dai shi ne Paul Manafort, tsohon daraktan yakin neman zaben shugaban, an same shi da laifufuka har guda 8, da suka hada da damfarar gwamnati ta hanyar kin biyan haraji, sai kuma Michael Chohen wanda aka sama da kaifin sarrafa kudaden yakin neman zaben shugaban ta hanyar da ta saba wa ka’ida.

Tun bayan nadi mai shigar da karar na musaman watanni 15 da suka gabata, Shugaba Donald Trump ke ci gaba da danganta binciken da yake gudanarwa a matsayin bita da kulli, har zuwa jiya laraba da ya ce yana kokarin ganin ya gurfanar da shi ne a gaban Kotu

A ganin manazarta dai duk wata nasara da M. Mueller da zai samu a wannan bincike ta na zama nasara ce kan shugaban Mr D Trump

Yanzu haka dai za a iya cewa, shugaba Trump na da jan aiki a gabansa a wajen shawo kan masu zabe a zaben yan majalisar dokokin watan November mai zuwa, domin ci gaba da kare rinjayen da yake da shi a majalisun dokokin kasar ta Amruka

A lokacin da yake maida martaninsa na farko a ranar talatar da ta gabata, shugaba Trump ya jadadda cewa a ganinsa binciken mai shigar da karar nan musaman ba ya da da wata hujja, domin shi cikin badakalar, domin babu wata alaka da badakalar shishigin Rasha a zaben kasar, illa ci gaba da yin masa bita da kulli da yake yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.