Isa ga babban shafi
Syria

Amurka ta dakatar da tallafin sake gina kasar Syria

Amurka ta ce ta dakatar da tallafin kudin dala miliyan 230 da aka tsara za’a yi amfani da su wajen sake gudanar da manyan ayyukan samar da ababen more rayuwa a Syria.

Daya daga cikin sassan birnin Douma, da ke yankin gabashin Ghouta, a birnin Damascus na Syria da yaki ya rusa. 30 ga Maris, 2018.
Daya daga cikin sassan birnin Douma, da ke yankin gabashin Ghouta, a birnin Damascus na Syria da yaki ya rusa. 30 ga Maris, 2018. REUTERS/Bassam Khabieh/File Photo
Talla

Sai dai gwamnatin Amurkan ta ce matakin ba wai yana nufin za ta janye kanta baki daya bane daga shirin sa ke gina kasar Syrian, za ta ci gaba da kasancewa cikin shirin, amma bisa sharadin za’a aiwatar da shi a karkashin yarjejeniyar da aka cimma cikin shekarar 2012 a birnin Geneva, wadda ta bukaci shugaban kasar Bashar Al-Assad ya mika mulki ga ‘yan adawa.

Sai dai gwamnatin kasar ta Syria da kawarta Rasha sun dade suna adawa da sharadin yarjejeniyar ta Geneva, wadda haryanzu babu alamun za su yi na’am da ita.

Matakin na Amurka ya zo ne a dai dai lokacin da shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel sun yi gargadin cewa, fararen hula a lardin Idlib na Syria na fsukantar hadarin afkawa cikin mummunan hali.

Shugabannin na Faransa da Jamus wadanda suka yi gargadin yayin ganawarsu ta wayar tarho, sun ce, lardin wanda ke karkashin ‘yan tawaye, ya kama hanyar zama wuri na gaba da za’a gwabza kazamin yaki, bayanda shugaba Bashar al-Assad ya sha alwashin shi ne yankin ‘yan tawaye na gaba da zai murkushe.

Lardin Idlib ya dade da zama matattarar dubban fararen hula, hadi da mayakan ‘yan tawayen kasar da kuma iyalansu, wadanda suka baro yankunan da suka mamaye a bayan, bayan cimma yarjejeniyar sake mika wasu yankunan kasar da dama ga gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.