Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya musanta masaniya kan ganawa da wakilan Rasha a 2016

Shugaban Amurka Donald Trump ya musanta zargin masaniya game da ganawar wasu makusantansa da wasu jami'an Rasha wadda ta kai ga tattaunawa kan yadda za a batawa abokiyar takararsa Hillary Clinton suna a zaben kasar na 2016.

Kalaman na Trump dai kai tsaye na nufin tsohon lauyan nasa Micheal Cohen wanda yanzu haka ke fuskantar tuhuma kan yadda ganawar ta gudana.
Kalaman na Trump dai kai tsaye na nufin tsohon lauyan nasa Micheal Cohen wanda yanzu haka ke fuskantar tuhuma kan yadda ganawar ta gudana. Reuters/路透社
Talla

Wasu hujjoji sun tabbatar da yadda sirikin Trump Jared Kushner da kuma dan Trump din Donald Junior da babban jami'in yakin neman zabensa Paul Manafort suka gana da lauyar Rasha Natalia Veselnitskaya ranar 9 ga watan Yunin 2016 suka gana a ginin Trump Tower wadda ta mika musu bukatar kasarta na taimakawa shugaban na Amurka kai wa ga nasara a zaben.

Ko da dai a lokuta da dama Trump na ci gaba da musanta masaniya kan ganawar wadda ya ce bada yawunsa aka yi ba, amma wasu gidajen talabijin a Amurkan na CNN da NBC sun tabbatar da cewa tsohon lauyan shugaban Micheal Cohen ya ce sai da Donald Junior ya sanar da mahaifin na sa ya kuma amince kafin suka yi ganawar.

a sakon da ya wallafa yau a shafinsa na Twitter Donald Trump ya ce bayada masaniya kan ganawar ta dansa da jakadan Rasha gabanin zaben, inda ya ce da alama wani na son tsame kan sa ne daga matsala shi ne shi ya ke son jefa shi.

Kalaman na Trump dai kai tsaye na nufin tsohon lauyan nasa Micheal Cohen wanda yanzu haka ke fuskantar tuhuma kan yadda ganawar ta gudana.

Tuni dai lauyan Trump a yanzu Rudy Giuliani ya shaidawa gidan talabijin na CNN cewa babu kanshin gaskiya a kalaman Cohen kuma ma koma ba komi Cohen ya yi kaurin suna wajen shirya karya da kagaggun labarai tsawon lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.