Isa ga babban shafi
Faransa

Jami'an tsaro sun wargaza sansanin baki a Paris

Jami’an ‘yan sanda a birnin Paris na Faransa sun wargaza wani sansanin ‘yan gudun hijira kwanaki kalilan bayan da masu bai wa marasa matsugunnai muhalli suka yi kashedin cewar, ana fuskantar matsala sakamakon hayaniyar da ake samu da kuma yawan sokawa juna wukake da ‘yan gudun hijirar ke yi.

Wasu 'yan gudun hijira da suka kafa sansaninsu a birnin Paris
Wasu 'yan gudun hijira da suka kafa sansaninsu a birnin Paris Foto: REUTERS/Charles Platiau
Talla

Sama da ‘yan gudun hijira 1000 ne aka kwashe da suka fito daga kasashen Somalia da Sudan da Eritrea, kuma wannan na zuwa ne kwana daya bayan da wani dan gudun hijirar daga Mali da ya shiga kasar ta barauniyar hanya ya ceci wani karamin yaro da ke gaf da fadowa daga hawa 4 na wani gidan bene a birnin Paris.

An kuma kwashe ‘yan gudun hijirar ne da ke a sansanin Millenair a kan yankin mabiyar ruwa ta Porte de la Villette a arewa maso gabashin birnin na Paris da ke dauke da ‘yan gudun hijira akalla 1,700.

Ba a dai samu wani tashin hankali a lokacin kwashe ‘yan gudun hijirar ba, saboda matakan tsaron da aka dauka.

Jami’an tsaron dai sun dauki hayar motoci ne domin dauke ‘yan gudun hijirar zuwa wasu gidajen wucen gadi, in da ake shirin ajiye ‘yan gudun hijrar.

Jagoran yankin na birnin Paris Mr. Collum ya bayyana cewar, haka ma akwai wasu kananan sansanoni da aka tanada domin adana ‘yan gudun hijirar da kusan kullun kan kwarara zuwa Turai domin neman kyakkyawar rayuwa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.