Isa ga babban shafi
Iran- Turai

Iran na tattaunawa da Turai kan nukiliyarta

Yau ne Ministan Harakokin Wajen Iran, Mohammad Javad Zarif ke tattaunawa da wasu kusoshin Kungiyar Tarayyar Turai a birnin Brussels a jerin ziyarar da ya fara a ranar Assabar daga kasar China zuwa Rasha ta neman mafita da kuma dorewar yarjejeniyar nukliyar da kasar ta cimma da kasashen Turai bayan ficewar Amurka daga cikinta.

Ministan Harkokin Wajen Iran, Mohammad Javad Zarif
Ministan Harkokin Wajen Iran, Mohammad Javad Zarif Reuters
Talla

Mr. Zarif ya fara ziyarar ne a ranar Assabar daga China, in da ya gabatar wa mahukumtan kasar korafin fcewar Amurka daga yarajejeniyar nukliyar 2015 tare da neman goyon bayan China wajen ci gaba da dorewarta, kafin ya zarce Moscow in da suka yi doguwar tattaunawa da takwaransa na Rasha, Sergei Lavrov kafin zuwansa birnin Brussels a yau Talata.

Kasashen Turai sun lashi takobin ganin sun ci gaba da aiki da yarjejeniyar duk da ficewar Amuruka daga cikinta.

Da farko dai Iran ta lashi takobin watsi da yarjejeniyar idan Amurka ta fice daga cikinta, amma daga bisani ta sassauta matsayinta ganin kasashen 5 da suka cimma yarjejeniyar da ita a 2015 da suka hada da Britaniya da Faransa da Jamus da Rasha da kuma China sun nuna rashin jin dadinsu da ficewar Amurkar ba tare da wata hujja ba ya sa ta sassauto ita ma domin samun masalaha a lamarin

Za a iya cewa shugaban Amurka Donald Trump ya cika alkawarin da ya dauka na fitar da kasar daga cikin yarjejeniyar kamar yadda ya alkawalta a yakin neman zabensa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.