Isa ga babban shafi
Amurka

Yau Amurka ke bude ofishinta a birnin Kudus

Yau kasar Amurka ke bude ofishin Jakadancinta a birnin Kudus duk da fargabar da kasashen duniya ke yi na cewar matakin ka iya dakushe shirin zaman lafiya tsakanin Israila da Falasdinu.

Kasashen duniya na adawa da matakin shugaba Trump na mayar da ofishin jakadancin Amurka daga Tel Aviv zuwa birnin Kudus
Kasashen duniya na adawa da matakin shugaba Trump na mayar da ofishin jakadancin Amurka daga Tel Aviv zuwa birnin Kudus REUTERS/Ronen Zvulun
Talla

Bude ofishin jakadancin na zuwa ne a dai dai lokacin da Isra’ila ke cika shekaru 70 da kafuwa, yayin da gobe Talata ake cika shekaru 70 da Falasdinawa suka  kaddamar da Nakba wadda ta yi sanadiyar raba kakaninsu sama da dubu 700 da gidajensu da kuma haifar da yaki.

Shugaba Donald Trump ba ya cikin wadanda za su halarci bikin bude ofishin a yau, amma ‘yarsa Ivanka da mijinta Jared Kushner za su halarta.

Ana saran shugaba Trump zai gabatar da jawabi ga wadanda suka halarci bikin na yau ta hanyar sadarwar hoton bidiyo daga Amurka.

A bara ne shugaba Trump ya sanar da aniyarsa ta mayar da ofishin jakadancin Amurka daga birnin Tel Aviv zuwa birnin Kudus, matakin da kasashen duniya ke kallo a matsayin wani bakon abu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.