Isa ga babban shafi

'Yan sandan Interpol sun kama ton 3,600 na gurbataccen abinci

Wani samamen hadin guiwa tsakanin hukumomin yan sandan kasa da kasa Interpol da ta turai Europol su ka aiwatar ya samu nasarar bankado manyan kungiyoyin bata gari kusan 50 dake safarar gurbatacen abinci da lalataciyar barasa zuwa kasuwanin kasashen duniya.

Wasu daga cikin jami'an 'yan sandan kasa da kasa na Interpol.
Wasu daga cikin jami'an 'yan sandan kasa da kasa na Interpol. Yahoo
Talla

A cikin sanarwar da hukumomin ‘yan sandan 2 suka fitar, sun bayyana samun nasarar kama sama da ton dubu 3, 600 na gurbatacen abinci mai hadari ga rayukan jama’a, da kuma lita miliyan 97 na gurbataciyar barasa aka kwace, da kuma aka kiyasta yawan kudin da cewa sun kai Euro miliyan 55

Hukumomin yan sandan na duniya sun bayana cewa sun samu nasarar wannan kamu ne, a cikin samamen da suka kaddamar daga ranar 1 ga watan Disambar bara zuwa 31 ga watan Maris din bana.

Wannan dai shi ne karo na farko da aka samu nasarar kama gurbatacen abinci da barasa mai tarin yawa a tarihin hukumomin, kamar yadda suka sanar.

A kasar Indonesia kawai ‘yan sanda sun yi nasarar kama gurbataciyar barasar da ta hallaka mutane 60 bayan da su ka kwankwadeta.

A Rasha kuma, kusan kamfanonin sarrafa barasa na bogi 50 aka bankado da kuma ke wakiltar samar da gurbataciyar barasar da yawanta ya kai lita miliyan 1.6 wanda hakan ya bada damar gurfanar da mutane 280 a gaban kuliya domin yi masu hukunci a kan laifin da suka aikata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.