Isa ga babban shafi
Canada

'Yan sandan Canada na binciken maharin Toronto

Jami’an ‘yan sandan Canada na gudanar da tambayoyi kan direban da ake zargi da kashe mutane 10 tare da raunata 15 bayan ya afka wa jama'ar da ke tafiya da kafa a gefen titi da motarsa.

Motar da aka yi amfani da ita wajen kai harin Toronto a Canada
Motar da aka yi amfani da ita wajen kai harin Toronto a Canada Cole Burston/Getty Images/AFP
Talla

Alek Minassian mai shekaru 15 da ake zargi da kisan jama’a da gan-gan na ci gaba da shan tambayoyi kan wannan harin.

Lamarin ya faru ne da ranar tsaka a jiya Litinin a wurin da ke da nisan kilomita 16 da in da ake gudanar da taron kasashen G7 masu karfin tattalin arzikin duniya.

Sai dai hukumomin kasar sun ce, babu wata sheda da ke nuna alakar harin da taron na G7.

An jinjina wa dan sandan da ya yi kokari wajen shawo kan maharin har ya mika kansa duk da cewa maharin ya shaida wa dan sandan cewa yana dauke da bindiga, amma jami’in ya nuna halin ko in kula.

Babu dai wata musayar wuta da ta gudana kafin cafke maharin.

Firaministan Canada, Justin Trudeau ya bayyana harin a matsayin na rashin hankali wanda kuma ya ce, ya haddasa masa mummunan bakin ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.