Isa ga babban shafi
Faransa

An tsare Bollore a birnin Paris kan badakalar cin hanci

Hukumomin Faransa sun tsare fitaccen Bafaranshen dan kasuwan nan a nahiyar Afrika, Vincent Bollore don ci gaba da bincike kan wata badakalar cin hanci da ta shafi kamfaninsa bayan ya samu kwantiragin tafiyar da tashoshin jiragen ruwa a yammacin Afrika.

Attajirin dan kasuwa Vincent Bollore na shan tambayoyi a birnin Paris kan badakalar cin hanci da rashawa a Guinea Conakry da Togo
Attajirin dan kasuwa Vincent Bollore na shan tambayoyi a birnin Paris kan badakalar cin hanci da rashawa a Guinea Conakry da Togo REUTERS/Charles Platiau
Talla

Attajirin mai shekaru 66 kuma shugaban gungun kamfanin Bollore ya shiga hannun hukumomi ne a yau Talata a birnin Paris don amsa tambayoyi kan yadda kamfaninsa ya samu kwantiragin tafiyar da tashar jirgin ruwa ta birnin Lome da ke Togo da kuma ta Conakry da ke Guinea kamar yadda wata kwarrarar majiya ta bayyana.

Tuni dai dan kasuwan ya musanta aikata ba dai dai ba kan abin da ake zargin sa da shi.

Rahotanni na cewa, labarin tsare babban dan kasuwan ya sa hannayen jarin Bollore sun fadi da fiye da kashi 8 a birnin Paris.

Kamfanin Bollore dai na gudanar da ayyukansa a fannin gine-gine da sufuri da kafafen yada labarai da tallace-tallace da kuma harkokin jiragen ruwa har ma da na jiragen kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.