Isa ga babban shafi
Rasha

Rasha ta kori jakadun kasashen Turai sama da 40

A martinin ramuwar gayya da ta ke mayarwa dangane da korar jami’anta fiye da 100 da kasashen Turai suka yi a farkon makon nan, Rasha ta sallami jami’an kasashe 18 galibinsu na Turai da yawansu ya haura 40.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

Rasha dai ta sallami hur-hudu daga jakadun kasashen Jamus da Poland, yayin da ta sallami uku-uku daga na Jamhuriyar Czech da Lithuania, sai kuma bib-biyu daga kasashen Italiya da Spain da Albania da Denmark.

Zalika Rashan ta sallami jakadu dad-dai da suka fito daga kasashen Latvia da Estonia da Croatia da Sweden da Romania da Ireland da Norway da kuma Finland.

A bangare guda kuma, ana kyautata zaton Faransa ma ka iya karbar korarrun jami’an akalla 4, ko da yake dai Rashan ba ta kai ga sanar da hakan a hukumance ba.

Tun kafin yanzu dai Rasha ta sallami akalla jakadun Birtaniya da Amurka amma duk da hakan a yau ta kara da sanar da yanke hulda tsakaninta da kasashen biyu.

A bangare guda kuma kasashen Slovakia da Malta da Bulgaria da Luxembourg sun kira jami’ansu da ke kasar ta Rasha don gyatta alaka, yayin da Bulgeria ta sanar da cewa ba za ta kori jami’an na Rasha ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.