Isa ga babban shafi
Rasha

Rasha za ta sallami jakadun Amurka 60

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya sanar da cewa kasarsa na gab da sallamar jakadun Diflomasiyyar Amurka akalla 60 tare ga rufe ofishin jakadancin Amurkan. Matakin dai na zuwa ne a matsayin martini kan korar jami'an Diflomasiyyan Rashan da Amurkan ta yi a farkon makon nan.

Shugaban Rasha Vladimir Putin dai a baya ya zargi Amurkan da tunzura kasashen yammacin Duniya don daukar matakin korar jami'an Diflomasiyyarta.
Shugaban Rasha Vladimir Putin dai a baya ya zargi Amurkan da tunzura kasashen yammacin Duniya don daukar matakin korar jami'an Diflomasiyyarta. Yuri Kadobnov/POOL via Reuters
Talla

Bayan daukar matakin sallamar jakadun Diflomasiyyar Rasha da kasashen yammacin duniya suka yi a ranar Litinin din da ta gabata kan zargin hannunta a yunkurin kisan tsohon jami'in leken asirinta da ya koma aiki da birtaniya, Rashan  ta zargi Amurka da tunzura kasashen duniya don daukar matakin korar jami'an na ta.

Tuni dai Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadin dawowar yakin cacar baka tsakanin kasashen yammacin duniyar da Rasha sakamakon zargin yunkurin kisan da ke kara zama dalilai na wargaza alakar kasashen duniya da Rasha.

A jawaban da ya gabatar gaban zaman majalisar na yau a birnin Newyork, Guteress ya ce alamu na nuni da cewa al'amura za su dawo baya kamar yadda ake a da, ta yadda kasashe za su rika yaki ta hanyar zafafan kalamai.

Amurka dai ita ce ta kori jami'an Diflomasiyyar Rasha mafi yawa.

Ko a shekarar 2016 ma,Tsohon shugaban Amurkan Barrack Obama ya sallami akalla jami'an Diflomasiyyar Rashan 35 kan zargin kutse a zaben kasar.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.