Isa ga babban shafi
Amurka

Rashin kudin gudanarwa ya tilastawa Amurka kulle ma'aikatu

Daruruwan ma’aikatan Amurka ne suka kauracewa zuwa wuraren ayyukansu a yau Litinin, a dai dai lokacin da majalisar dattijan kasar ke ta kokarin kawo karshen karancin kudin gudanarwar da gwamnatin kasar ke fuskanta. Kawo yanzu dai, Amurka ba ta da kudaden biyan daruruwan ma’aikata albashi lamarin da ya tilasta kulle ma'aikatun har zuwa lokacin da za a kawo karshen matsalar.

Shugaban Amurka Donald Trump ya shafe kusan dukkanin hutunsa na karshen mako a Ofis don shawo kan majalisun kasar su amince da kudurin samar da kudaden gudanarwa ga gwamnatinsa.
Shugaban Amurka Donald Trump ya shafe kusan dukkanin hutunsa na karshen mako a Ofis don shawo kan majalisun kasar su amince da kudurin samar da kudaden gudanarwa ga gwamnatinsa. REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Bangarorin jam’iyyar Democract da Republican na ci gaba da zargin junansu a matsayin ummul aba'isin matsalar, yayinda majalisar dattijan kasar ke shirye-shiryen wani zama na musamman a yammacin yau Litinin don kada kuri’a kan kudurin shugaban kasar Donald Trump wanda zai samarwa gwamnatin kudaden gudanarwa cikin sauri.

Matsalar ta karancin kudin gudanarwar gwamnati za ta shafi ma’aikatan bangaren gidaje da na muhalli da bangaren ilimi wadanda dukkaninsu za su kasance a gida ba kuma tare da biyansu kudaden ranakun da suka kasance a gidan ba, ko da bayan farfadowar gwamnatin.

Haka zalika matsalar za kuma ta shafi kaso hamsin cikin dari na ma’aikatan bangaren kudi dana lafiya da tsaro da sufuri.

A bangare guda kuma Ma’aikatun tsaron kasa da na rarraba wasiku da ma’aikatar da ke kula da zirga-zirgar jiragen sama da wani bangre na ma'aikatar lafiya da ma’aikatar kula da bala’o’I da ta gidan yari da ta karbar haraji da ma’aikatar lantarki za su kasance a bude.

A shekarar 2013 Amurka ta fuskanci makamanciyar wannan matsala ta tsawon kwanaki 16 lamarin da ya tilasta kulle daruruwan ma’aikatu ba kuma tare da biyan ma’aikatan albashinsu na tsawon ranakun ba.

Tuni dai shugaban kasar Donald Trump ya bukaci a bude dukkanin gidajen shakatawar ba dare ba rana don amfanin mutanen da ba za su je aiki ba, lamarin da ya harzuka al'ummar kasar da dama.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.