Iran na mutunta yarjejeniyar nukiliya ta 2015
Masu bincike na hukumar hana yaduwar makaman nukiliya a duniya, sun ce Iran ta mutunta dukkanin sharuddan da ke kunshe a yarjejeniyar nukiliyar da ta kulla da kasashen duniya a shekara ta 2015.
Wallafawa ranar:
Rahoton da hukumar ta IAEA ta fitar ya ce, binciken watanni hudu-hudu da aka saba gudanarwa, ya tabbatar da cewar har yanzu ba inda kasar ta saba wa sharuddan da aka gindaya mata.
Bayanan na IAEA ya zo ne a daidai lokacin da Amurka ke cewa akwai bukatar aikewa da masu bincike zuwa barikokin sojin Iran domin tabbatar da cewa ba ta gudanar da ayyukan nata na nukiliya a boye.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu