Isa ga babban shafi
Iran

Iran ta mayar da martini kan takunkumin Amurka

Iran, ta danganta sabin takunkuman da Amruka ta kakaba mata a matsayin taka yarjejeniyar nukliyar da ta cimma da kasashen duniya, tare da yin barazanar mayar da zazzafan martini kan Amruka. Hakan na zuwa ne a dai dai lokacin da shugaban kasar Hasan Rohani ke fara aiki a hukumance cikin sabon wa’adinsa na 2 na sugabancin kasar.

Shugaban kasar Iran Hassan Rohani
Shugaban kasar Iran Hassan Rohani REUTERS/Mike Segar
Talla

A lokacin wasu shagulgulan hukuma ne jagoran addini a kasar Ali Khamenei ya tabbatarwa Hassan Rohani, nasarar zaben da aka yi masa, wani mataki mai matukar muhimmanci a karkashin doka dake buda sabon babin farawar wa’adi na biyu ga shugaba Rohani.

A ranar asabar mai zuwa ne dai shugaba Hassan Rohani mai sassaucin ra’ayi zai sha rantsuwar fara aiki a majalisar dokokin kasar.

Duk da gagarumin rinjayen da ya samu a zaben, Hassan Rohani na ci gaba da shan sukar cikin gida, inda masu ra a yin yan mazan jiya ke zarginsa da mika wuya sosai ga manyan kasashen duniya, tare da kin saurarensu kan kashedin da suke yi wa Amruka babbar abokiyar adawar kasar ta Iran.

Yarjejeniyar nukiliyar watan Yulin 2015 da aka sakawa hannu tsakanin Tehran da kasashen Faransa da Birtaniya, Rasha da Sin da kuma Jamus, ta bukaci takaita shirin samar da makamashin nukliyar Iran, a yayinda ita kuma za a cire mata takukuman kariyar tattalin arizikin da kasashen duniya suka kakaba mata.

Sai dai kawo yanzu sabanin gwamnatin shugaba Barack Obama da ta gabata a Amruka, gwamnatin shugaba Donald Trump na ci gaba da nuna halayen tsokana ga kasar ta Iran, al’amarin da ke barazana ga yarjejeniyar nukliyar da aka cimma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.