Isa ga babban shafi
Philippines

'Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane a Philippines

Wasu mayaka, masu tsattsauran kishin Islama sun yi wa wata makarantar Firamare da ke kudancin Philippines kofar rago, in da suka yi garkuwa da fararen hula.

'Yan bindiga sun yi garkuwa da fararen hula a wata makarantar Firamare da ke kudancin Philippines
'Yan bindiga sun yi garkuwa da fararen hula a wata makarantar Firamare da ke kudancin Philippines REUTERS/Stringer
Talla

Gabanin wannan garkuwa, daruruwan ‘yan bindiga sun far wa wani sansanin sojoji da asubahin wannan Laraba, kafin daga bisani su yi wa makarantar kofar rago tare da yin garkuwa da fararen hula.

Mai Magana da yawun sojin Philippines, Kaften Arvin Encinas ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa, har yanzu, mayakan na ci gaba da tsare fararen hular.

Encinas ya kara da cewa, ‘yan bindigan sun kuma dasa bama-bamai a kewayar makarantar, amma an baza sojoji a kusa da makarantar ta kananan yara.

Rahotanni sun ce, kimanin mutane 20 ne masu makwabtaka da makarantar aka yi garkuwa da su, amma babu dalibi ko guda a cikinsu kamar yadda hukumomin kula da harkar ilimi ta kasar suka sanar.

Wannan lamarin dai ya faru ne a wani karamin kauye da ya shahara ta fannin noma wanda kuma ke da tazarar kilomita 160 daga birnin Marawi, in da mayakan da ke da alaka da kungiyar ISIS suka shafe tsawon wata guda suna dauki ba dadi da sojoji, abin da ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan jama’a.

Ana ganin garkuwar ta yau, wata dabara ce ta fautar da hankulan sojojin daga yakin birnin Marawi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.