Isa ga babban shafi
Philippines

Ana fargabar samun karuwar harin bama-bamai a Philippines

Shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte, ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar a cigaba da samun fashewar bama-bamai a kasarsa, saboda aniyar daukar fansa da wasu ke da ita kan gwamnatinsa. 

Shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte tare da sojojin kasar
Shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte tare da sojojin kasar REUTERS/Lean Daval Jr
Talla

Duterte ya yi wannan gargadi ne sati daya, bayan da aka kai wani harin bam a kasar, wanda ya halaka mutane 14 da raunata wasu 60.

Ko da yake shugaban na Philippines bai bayyana sunan kungiyar da ta kai harin ba, tuni aka aike da jami’an soja 7,000 yankin Sulu da ke kasar inda mayakan Abu Sayyaf ke da karfi, wadanda kuma ake zargin sune suka kai harin bam din da ya halaka mutane 14 a kasar.

A wata sanarwa data fitar rundunar sojin ta ce ta kashe mayakan na Abu Sayyaf 32, wadanda suka yi mubaya’a ga kungiyar ISIL a kwanakin da suka gabata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.