Isa ga babban shafi
Philippines

Abu Sayyaf ce ta kai harin Philippines

Magajiyar garin Davoa da ke kasar Philippines Sara Duterte, ta bayyana kungiyar ‘yan tawaye ta Abu Sayyaf a matsayin wadda ta kai harin bam a wata kasuwa da ke garin, abinda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 14 tare da jikkata kusan 70.

Garin Davoa da aka kaddamar da farmakin bam a Philippines
Garin Davoa da aka kaddamar da farmakin bam a Philippines REUTERS/Lean Daval Jr
Talla

Ita ma ma’aikatan tsaron kasar ta yi amanna cewa, kungiyar ta Abu Sayyaf wadda ta yi mubaya’a ga ISIS ce ta kai farmakin.

A makon jiya, shugaban kasar Rodrigo Duterte ya bayar da umarnin fatattakar ‘yan kungiyar a maboyarsu da ke tsibirin Jolo mai tazarar kilomita 900 daga Davoa, mahaifar shugaban.

Rahotannin sun ce, kimanin sojojin kasar 15 ne suka mutu a rangamar da kungiyar a ranar litinin.

An kai harin na jiya ne a dai dai lokacin da shugaba Duterte ke ziyara a garin, amma yana nesa da ksuwar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.