Isa ga babban shafi
Amurka

Ana binciken Trump kan yunkurin hana binciken kutsen Rasha

Kwamitin da ke binciken kutsen da Rasha ta yi wa zaben Amurka na diba yiyuwar soma binciken shugaba Donald Trump kan yunkurin boye gaskiya tare da hana adalci a binciken.

Donald Trump shi ne shugaban Amurka na 45
Donald Trump shi ne shugaban Amurka na 45 ©REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Za a binciki ko Trump ya yi kokarin kawo karshen binciken na Rasha bayan ya tube mai ba shi sharawa kan sha’anin tsaro da kuma shugaban hukumar FBI.

Jaridar Washington Post ta Amurka ta ruwaito cewa babban jami’in leken asiri ya amince ya gurfana gaban masu bincike domin tattaunawa da shi akan ko shugaba Trump ya yi kokarin kawo karshen binciken kutsen Rasha a zaben shugaban kasa da ya yi nasara.

A rahoton da Jaridar ta wallafa ta ambato manyan jami’an leken asirin Amurka 5 da suka amince a tattauna da su da suka hada da shugaban NSA da kuma tsohon mataimakinsa.

A nata bangaren jaridar New York Times ta ruwaito cewa jagoran binciken Robert Mueller ya nemi wasu muhimman takardu da suka shafi bayanai tsakanin NSA da gwamnatin Trump kan batun zargin Rasha ta taimakawa yakin neman zaben shugaban.

Ana dai zargin Trump da yunkurin hana ci gaba da gudanar da binciken tare da matsin lamba ga hukumar FBI na ta jingine bincike akan tsohon mai ba shi shawara kan sha’anin tsaro Mike Flynn.

Trump ya mayar da martani a twitter inda ya danganta labarin a matsayin na karya tare cewa ana masa bita da kulli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.