Isa ga babban shafi
Najeriya-Indonesia

Najeriya ta bukaci janye hukuncin kisa kan 'yan kasar

Gwamnatin Najeriya ta roki Indonesia da ta yi wa Allah ta sauya hukuncin kisan da ta yanke wa 'yan Najeriya 50 zuwa daurin rai da rai.

Kimanin 'yan Najeriya 300 na dakon hukuncin kisa a yankin Asiya saboda safarar miyagun kwayoyi
Kimanin 'yan Najeriya 300 na dakon hukuncin kisa a yankin Asiya saboda safarar miyagun kwayoyi AFP/STR
Talla

Ministan Harkokin Wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya gabatar da bukatar a ganawar da suka yi da takwararsa ta Indonesia Retno Marsudi.

Kungiyoyin kare hakkin Bil Adama sun bukaci gwamnatin Najeriya da ta kara kaimi wajen ganin an kubutar da 'yan kasar da ke jiran a aiwatar mu su da hukuncin kisan.

Kungiyar LEDAP ta ce, akalla 'yan Najeriya 300 ke jiran a aiwatar mu su da hukuncin kisa a kasashen Asia sakamakon samun su da laifin safarar miyagun kwayoyi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.