Isa ga babban shafi
Koriya ta Arewa

Koriya ta Arewa ta yi gwajin makami na 12 a bana

Koriya ta Arewa ta sake harba wani makami mai linzame a sanyin safiyar yau Litinin, irinsa na uku a cikin makwanni biyu, kuma na 12 a cikin wannan shekara duk da kuwa da kudororin Majalisar Dinkin Duniya da ke haramta yin haka.

Koriya ta Arewa ta sake gwajin makami mai linzame mai cin gajeren zango
Koriya ta Arewa ta sake gwajin makami mai linzame mai cin gajeren zango REUTERS
Talla

Ma’aikatar tsaron Amurka ta tabbatar da yin gwajin wadda ta ce an yi da makami mai cin gajeren zango, yayin da Japan ta ce makamin ya fada a cikin wani yankin ruwan teku mallakinta.

Japan ta ce gwajin makamin duk da cewa bai fado kan kowa ba amma barazana ne ga jiragen sama.

Firaministan Japan Shinzo Abe wanda ya yi allawadai da gwajin ya shaidawa manema labarai cewa ba za su bari Koriya ta Arewa na yi wa duniya barazana ba.

Shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-In ya kira wani taron gaggawa na Majalisar tsaron kasar domin nazari kan gwajin makamin da Koriya ta arewa ta yi.

Gwamnatin Donald Trump na Amurka ta yi alkawalin hawa teburin tattaunawa da Koriya ta Arewa amma idan za ta dakatar da gwajin makamanta na Nukiliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.