Isa ga babban shafi
Sri Lanka

Mutane 151 suka mutu a Ambaliyar ruwan sama a Sri Lanka

Yau Lahadi masu ayyukan agaji a kasar Sri Lanka na cigaba da ayyukan ceto sakamakon mummunar ambaliyar ruwan sama da ta shafi mutane samada dubu 500 da suka rasa muhalli. 

Wasu wurare da aka sami hasara a ambaliyar ruwan sama a Sri Lanka
Wasu wurare da aka sami hasara a ambaliyar ruwan sama a Sri Lanka REUTERS/Dinuka Liyanawatte
Talla

Mamata dai ya zuwa yanzu sun haura 151 yayin da wasu mutanen 111 har yanzu babu duriyar su, wasu akalla 95 na kwance a Asibiti.

Gidajen mutane kusan dubu biyu suka rushe, a wannan ambaliyar ruwan sama da basu taba ganin irin ta ba samada shekaru 14 da suka gabata.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.