Isa ga babban shafi
Duniya

Koken Albashi ya mamaye ranar ma'aikata ta duniya

Yau daya ga watan Mayu ita ce ranar ma’aikata ta duniya, ranar da ta samo asali kimanin shekaru 131 da suka gabata.

Yau ce ranar ma'aikata ta duniya
Yau ce ranar ma'aikata ta duniya NLC
Talla

Ranar kan yi nazari tare da yin dubi a game da matsalolin da ma’aikata a karkashin gwamnatoci ko kuma kamfanoni masu zaman kansu ke cin karo da su a rayuwa.

A Najeriya dai batun karin kudin albashi shi ne babban abin da ma’aikata ke bukata daga gwamnati, kamar dai yadda shugabanni kungiyoyin ma’aikatan kasar suka jimma suna koke a kai.

Sakatare-Janar na kungiyar Kwadago a kasar Peter Ozon-Eson ya ce Naira dubu 18 a mastayin albashi mafi karanci babu inda zai kai ma’aikaci.

Yana mai cewa rashin albashi mai tsoka na daga cikin manyan matsalolin da ke addabar ma’aikata.

A cewar Sakataren Kungiyar Kwadagon Ma’aikata za su kalubalanci Gwamnonin jihohi da suka ki biyan dimbin ma’aikatansu albashi na tsawon watanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.