Isa ga babban shafi
Rasha

Rasha ta gargadi Amurka game da Koriya

Rasha ta gargadi Amurka da ta kauce wa yin gaban kanta wajen kai wa Koriya ta Arewa hari, jim kadan bayan da mataimakin shugaban Amurka Mike Pence ya sanar da cewa Pyongyang na dab da kure hakurin gwamnatin Donald Trump.

Mataimakin shugaban Amurka Mike Pence
Mataimakin shugaban Amurka Mike Pence Reuters
Talla

Mista Pence ya yi wannan gargadi ne a taron manema labaran da ya gabatar a yau litinin a birnin Seoul inda ya ke ziyara daidai lokacin da ake ci gaba da takun-saka tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa.

Mataimakin shugaban na Amurka ya sake jaddada matsayin kasar cewa, ‘akwai yiyuwar yin amfani da kowane irin mataki akan Koriya’’ sakamakon abin da Amurkan ta kira tsokana ta hanyar gwajin makamai musamman daga lokacin da Donald Trump ya dare kan karagar mulki.

A cikin makwanni biyu da suka gabata, Amurka ta kai hare-hare a wasu kasashe da suka hada da Syria da kuma Afghanistan, wata alama da ke nuni da cewa ana iya daukar irin wannan mataki a kan duk wata kasar da ke kokarin wuce gona da iri a cewar MikePence.

Sai dai ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya ce ba sa goyon bayan gwajin makamai da Koriya ta Arewa ke yi, amma ba za su amince da daukar mataki irin na gaba-gadi akan kasar ta kasar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.