Isa ga babban shafi
Afghanistan-Amurka

Amurka ta kashe mayan ISIS 90 a Afghanistan

Mahukuntan Afghanistan sun bayyana cewa, alkaluman Mayakan ISIS da Amurka ta kashe a wani hari da ta kai mu su sun kai 90 a wannan Asabar.

A karon farko kenan da Amurka ta yi amfani da irin wannan bam mafi girma a filin daga.
A karon farko kenan da Amurka ta yi amfani da irin wannan bam mafi girma a filin daga. Handout / US AIR FORCE / AFP
Talla

Amurkan dai ta yi amfani da bam dinta mafi girma wanda ba na nukiliya ba akan maboyar ‘yan kungiyar da ke gabashin kasar Afghanistan, matakin da ake kallo a matsayin daukar fansa dangane da kashe wani jami’in sojin kasar guda.

Wannan bam da aka bayyana cewa nauyinsa ya fi kilogram dubu 10, Amurka ba ta taba yin amfani da shi a fagen daga ba sai a wannan karo.

A farko dai, mahukuntan Afghanistan sun ce, mayakan ISIS 36 aka kashe a harin, yayin da shugaban kasar Ashraf Ghani ya nuna goyon bayansa game da farmakin kan kungiyar ta 'yan ta'adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.