Isa ga babban shafi
Syria

Harin makami mai guba ya kashe mutane 58 a Syria

Akalla mutane 58 da suka hada da kananan yara 11 sun rasa rayukansu sakamakon wani makami mai guba da aka yi amfani da shi wajen kaddamar da farmaki a yankin da ‘yan tawaye ke da iko da shi a arewa maso yammacin Syria.

Fararen hula ne dai harin na makami mai guba ya fi ritsa da su a Syria
Fararen hula ne dai harin na makami mai guba ya fi ritsa da su a Syria REUTERS/Muzaffar Salman/Files
Talla

Kungiyar da ke sanya ido kan hakkin bil’adama a kasar ta ce, jiragen yakin gwamnatin Syria ko kuma na Rasha ne suka kaddamar da farmaki a garin Khan Sheikhoun a safiyar yau Talata, abin da ya haddasa matsalar numfashi ga dimbin fararen hula.

Majiyoyin kiwon lafiya sun ce, wasu daga cikin mutanen da harin ya ritsa da su sun yi ta kwarara amai da suma da kuma fitar da kumfa daga baki.

Gwamnatin Syria dai na ci gaba da musanta amfani da makami mai guba wajen kai farmaki a kasar.

Wani bincike da Majalisar Dinkin Duniya da kuma Hukumar Haramta Amfani da Makami Mai Guba suka gudanar a cikin watan Oktoban bara, ya bayyana cewa, dakarun Syria sun yi amfani da sinadarin Chlorine a matsayin makamin yaki har sau uku a shekarar 2014 da 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.