Kasashen kawance na cikin shiri domin kawo karshen kungiyar IS
Kasashen kawance da ke yakar mayakan IS za su kaddamar da farmakin karshe na kakkabe mayakan daga cibiyarsu da ke Raqa a Syria sanarwa daga rundunar sojin kasashen .
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ministan tsaron faransa Jean-Yves Le Drian dake tabbatar da wannan yunkuri, ya ce farmakin zai kasance mafi girma da za a kaiwa IS don gani an kawo karshan su a Syria, kamar yadda ake fafatawa da su a Mosul na Iraqi.
IS na fuskantar farmaki daga bangarori da dama a arewacin Syria, inda Rasha ke bai wa dakarun Shugaba Assad cikakken goyon baya, a bangare guda kuma Turkiya na taimakawa kungiyoyin ‘yan tawaye dake yakar Mayakan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu