Isa ga babban shafi
Rasha

Dan asalin Kyrgyzstan ne ya kai harin Rasha

Hukumomin tsaron Kyrgyzstan sun bayyana wani dan asalin kasar a matsayin dan kunar bakin waken da ya hallaka mutane 11 a harin da ya kai a tashar jirgin karkashin kasa da ke Saint Petersburg na Rasha .

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ajiye firanni a wurin da aka kai harin St. Petersburg
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ajiye firanni a wurin da aka kai harin St. Petersburg REUTERS/Grigory Duko
Talla

Mai magana da yawun hukumar tsaron Kyrgyzstan ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa, Akbarjon Djalilov da aka haifa a shekarar 1995 ne ya kai harin na Rasha.

Wannan na zuwa ne a yayin da Rasha ta kaddamar da bincike don gano wadanda ke da hannu a harin wanda Majalisar Dinkin Duniya da Amurka suka yi Allah-wadai da shi.

Shugaba Vladimir Putin da ke St. Petersburg lokacin da aka kai harin, ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, in da ya ajiye firanni, amma ya ki cewa komai akai.

Hukumomin Rasaha sun ce, suna daukar harin a matsayin na ta’addanci.

Shugaban Amurka Donald Trump ya tattauna da Putin ta waya, in da ya jajanta ma sa abin da ya faru kafin shugabanin biyu suka kuma bayyana aniyarsu ta ci gaba da yaki da ta’addanci.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana harin a matsayin abin takaici, in da ya bukaci hukunta wadanda suka kitsa shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.