Isa ga babban shafi
Birtaniya

'Yan sandan Birtaniya sun kame mutane 8 a Birmingham

Mutane 5 aka tabbatar da mutuwar su yayin da wasu 40 suka samu raunuka sakamakon harin da wani mutum ya kai kusa da Majalisar Birtaniya, ya kuma dabawa wani dan sanda wuka. 

Jami'an 'yan sanda cikin shirin ko ta kwana a wajen harabar Majalisar dokokin majalisar Birtaniya.
Jami'an 'yan sanda cikin shirin ko ta kwana a wajen harabar Majalisar dokokin majalisar Birtaniya. REUTERS/Stefan Wermuth
Talla

Firaminista Theresa May tayi Allah wadai da harin wanda tace an kai shi ne a tsakiyar birnin London, inda ake da tarin mutane daga kasashe da addinai da kuma al’adu daban daban wadanda ke cikin walwalar ‘yanci na dimokiradiya.

A nashi sakon, Magajin Garin birnin London Sadiq Khan, yace wadanda ke kokarin gurbata rayuwar su, ba zasu taba cin nasara ba.

Tuni dai ‘yan sandan kasar sun kame mutane 8 a wani samame da suka kai a Birmingham, awanni bayan harin ta’addancin da aka kai a harabar majalisar dokokin kasar, inda mutane 5 suka rasa rayukansu, wasu 40 kuma suka jikkata.

Koda yake rundunar yan sandan kasar ta ki alakanta kai samamen da harin ta’addancin da ya auku, kafofin yada labaran kasar sun ce matakin yana da nasaba da kai harin.

A zantawarsa da sashin hausa na RFI, Dr Musa Aliyu na Jami’ar Coventry ya ce harin zai iya haifarwa da al’ummar Musulmi da ke kasashen turai ciki har da Birtaniya fuskantar tsangwama daga wasu, wanda kuma tun asali kowa ya san yadda al'ummar Musulmin ke zaune lafiya da abokan zamansu ba tare da tsangwama ba.

A cewar Dr Aliyu, tuni dama aka fara samun wasu da kan yi batanci ga Musulmi a nahiyar turan sakamakon alakantasu da ake yi da wadanda suke kai hare haren ta'addancin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.