Masana sun bayyana wasu hadduwan kamuwa da cutar Ebola
Masana harkokin kiwon lafiyar jama’a sun gano cewa mutanen da suka rayu bayan sun yi fama da cutar Ebola, na iya fuskantar matsaloli lafiyar jikin su nan gaba.
Wallafawa ranar:
Masanan na bayyana haka ne bayan sun gudanar da wasu gwaje-gwaje a kasar Guinea inda suka gano cewa ala tilas sai duk wanda ya taba kamuwa da cutar kuma ya warke sai ya cigaba da kai kansa wajen likitoci suna duba lafiyarsa.
Bayan gudanar da binciken masanan sun bayyana cewa kusan mutun daya daga cikin mutane 4 da suka taba kamuwa da wannan cuta har suka warke an gano cewa suna fama da ciwon gabobi, yayinda kashi 35% na fama da ciwon kai, kashi 22% kuma na fama da ciwon ciki.
An tsara gudanar da binciken cutar Ebola ne a kasar Guinea na tsawon shekaru biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu