Isa ga babban shafi
Amurka

Obama ya gabatar da jawabin ban-kwana

Shugaba mai barin gado Barack Obama, ya gabatar da jawabin karshe a matsayinsa na shugaban Amurka, jawabin da ya gabatar mai sosa zukata a gaban dimbin jama’a a birnin Chicago.

Barack Obama ya yi jawabin ban-kwana a matsayinsa na shugaban Amurka a Chicago
Barack Obama ya yi jawabin ban-kwana a matsayinsa na shugaban Amurka a Chicago REUTERS/John Gress
Talla

Obama wanda ke tare da matarsa Michelle da kuma mataimakinsa Joe Biden, ya tabo batutuwa da dama da suka faru a lokacin mulkinsa na shekaru 8, da suka hada samar da yarjejeniyar Nukiliya tsakanin kasashen duniya da Iran, da shirinsa na kiwon lafiya ga Amurkawa, tare da kuma karfafa gwiwar magoya bayan jam’iyyarsa ta Democrat bayan sun sha kayi a zaben da ya gabata.

Har ila yau shugaban mai barin gado ya yi kakkausar suka ga masu nuna wariyar jinsi, wadanda ya ce ra’ayinsu ya yi hannun riga da tsarin Dimokuradiyya.

A yayin jawabin Obama ya ce, "A cikin kwanaki 10 masu zuwa, duniya za ta shaidi kwarewarmu a game da Dimukuradiyya, za mu yi hakan ne ta hanyar mika mulki ta ruwan sanyi daga hannun shugaba mai ci zuwa ga shugaban da al’umma ta zaba."

"Zan mika ragamar mulki a hannun shugaba Trump kamar dai yadda shugaba Bush ya mika mulkin a hannuna. To amma ya kamata a san da cewa Dimokuradiyya na nufin nuna kauna a tsakanin juna." in ji Obama.

Shugaban ya jadda cewa, za su iya samar da sauyi a Amurka kamar yadda ya fadi a lokacin yakin neman zabensa shekaru 8 da suka gabata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.