Isa ga babban shafi

Hollande zai ziyarci ‘Yan tawayen FARC

Shugaba Francois Hollande na Faransa ya ce zai kai ziyara a yankin tsoffin ‘yan tawayen FARC na Colombia domin jaddada goyon bayansa ga yarjejeniyar da aka kulla tsakanin kungiyar da kuma gwamnatin Juan Manuel Santos.

Shugaban Faransa François Hollande
Shugaban Faransa François Hollande REUTERS/Lionel Bonaventure
Talla

Kafin wannan sanarwa, jakadan Faransa a kasar Jean Marc Laforet ya ziyarci yankin Elvira inda aka tattara tsoffin ‘yan tawayen FARC, inda ya ce kasar za ta ci gaba da taimakawa domin aiwatar da yarjejeniyar da bangarorin biyu suka kulla a watannin baya.

Tun dai lokacin da aka fara tattaunawar samar da zaman lafiya, Faransa ta kasance mai goyon bayan wannan shiri.

Hollande ya ce Fatan Faransa shi ne bayan kulla wannan yarjejeniya a shiga mataki na gaba, na fara cika alkawullan da kowane bangare ya dauka.

Shugaban ya kuma ce Faransa za ta ci gaba da bai wa Colombia gudunmuwa ta fannoni da dama, domin tabbatar da bukatun yarjejeniyar da kasar ta kulla da ‘yan tawaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.