Isa ga babban shafi
Colombia

Santos na Colombia ya lashe kyautar Nobel

Shugaban kasar Colombia Manuel Santos ya samu kyautar yabo ta zaman lafiya ta Nobel wadda aka sanar a yau juma’a, kuma an ba shi kyautar ne sakamakon namjin kokarinsa wajen samar da zaman lafiya ta hanyar kulla yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyar ‘Yan tawayen FARC.

Shugaban Colombia, Juan Manuel Santos
Shugaban Colombia, Juan Manuel Santos Fuente: Reuters.
Talla

Santos ya ce ya sadaukar da kyautar zuwa ga illahirin mutanen da wannan yaki na tsawon shekaru 52 ya shafa a kasar.
Jagoran ‘yan tawayen na FARC Timoleon Jimenez ya jinjina wa shugaban saboda wannan yabo da ya samu.

Lambar yabon ga Shugaba Santos dai ana ganin mataki ne da zai kara wa gwamnatin Colombia da ‘Yan tawaye kwarin guiwar ci gaba da mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta domin tabbatar da zaman lafiya a kasar.

A ranar 26 ga Satumba ne bangarorin biyu suka sanya hannu ga yarjejeniyar tsagaita wutar bayan shafe shekaru hudu suna tattaunawa.

An shafe shekaru sama da 50 Gwamnatin Colombia na fada da ‘Yan tawayen FARC, rikicin da ya lakume rayukan mutane sama da 260,000 tare da tursasawa sama da mutane miliyan bakwai kauracewa gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.