MDD za ta binciki laifukan yaki a Syria
Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shirin kafa wani kwamiti da zai tattara bayanan aikata laifukan yaki a Syria.
Wallafawa ranar:
Wannan dai wani yunkuri ne na ganin an hukunta wadanda suka aikata laifuka a yakin kasar da aka kwashe kusan shekaru 6 ana gwabzawa.
Kudirin da Liechestein ta gabatar tare da kasashe 58, cikinsu har da Amurka da Faransa da Birtaniya da Jamus da kuma Saudi Arabia, ya samu goyan bayan kasashe 105 a babban zauren Majalisar, yayin da 15 suka ki nuna goyon bayansu, in da kuma 52 suka ki kada kuri’a.
Ana saran kwamitin ya yi aiki da kwamitin binciken da aka kafa a baya wanda ya yi bayani kan yadda aka rika cin zarafin dan Adam a yakin da yanzu haka ya lakume rayukan mutane sama da 310,000.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu