Isa ga babban shafi
Syria-Rasha

Majalisar Dinkin Duniya zata tura masu sa ido zuwa Aleppo

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai yi zama kan wani kuduri da Faransa ta gabatar kan tura ‘yan kallo na kasashen duniya zuwa birnin Aleppo na Syria, to sai dai wasu bayanai na nuni a cewa ita ma Rasha da ke mara wa Bashar Assad baya, za ta gabatar da nata kudirin kan wannan batu.

Tawagar motocin Safa da suka fara kwashe mutane daga gabashin Aleppo
Tawagar motocin Safa da suka fara kwashe mutane daga gabashin Aleppo Reuters/路透社
Talla

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da aikin kwashe ‘yan tawaye da sauran fararen hula daga birnin na Aleppo.

Rasha dai ta yi barazanar hawan kujerar na-ki, domin tabbatar da cewa kudurin na Faransa bai yi nasara ba, to sai dai bayan wani taron sirri na tsawon awannin hudu da aka yi tsakanin kasashen da ke cikin kwamitin na sulhu, an yi wa daftarin na faransa gyaran fuska.

Babbar manufar daftarin na Faransa dai ita ce samar da ‘yan kallo na kasa da kasa da za su sa-ido kan yadda aikin kwashe ‘yan tawayen daga Aleppo ke gudana. Jakadan Faransa a Majalisar Francois Delattre ya ce tattaunawar da suka yi a asirce ta sa an samu fahinta a tsakanin kasashen.

Da misalin karfe biyu na rana agogon Najeriya ne ake sa-ran kwamitin sulhun zai kammala zamansa tare da fatan amincewa da wannan kuduri.

A dai ci gaba da aikin kwashe ‘yan tawaye da sauran fararen hula daga Aleppo yau Litinin, to sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga a kusa da birnin Idlib, sun kai hari tare da kona motoci da dama da aka tsara za a yi amfani da su domin kwashe fararen hular.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.