Isa ga babban shafi
Syria

An maido da shirin ficewar 'yan tawayen Aleppo

Gwamnatin Syria ta bayyana cewa, an cimma sabuwar yarjejeniya don bai wa 'yan tawaye damar ficewa daga yanki na karshe da suke rike da shi a birnin Aleppo.

Fararen hula na cikin tsaka mai wuya a Aleppo
Fararen hula na cikin tsaka mai wuya a Aleppo AFP
Talla

Wani babban jami'in sojin Syria ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, tuni aka fara shirye-shirye ficewar 'yan tawayen a yau Alhamis.

Sai dai jami'in bai yi bayani ba game da kwashe fararen hular da ke cikin tsaka mai wuya a birnin, amma 'yan tawayen sun tabbatar da  shirin kwashe fararen hular bayan rushewar wanda aka shirya a jiya.

Daya daga cikin shugabanin kungiyar 'yan tawayen Nureddine al-Zinki, wato Yaseer al-Youssef ya ce, an kulla sabuwar yarjejeniyar ce tsakanin kungiyar agaji ta Red Cross na kasashen Rasha da Turkiya, kuma sun amince da shirin.

Rahotanni sun ce shugaba Vladimir Putin na Rasha da Recep Tayyip Erdogan na Turkiya duk sun amince da shirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.