Isa ga babban shafi
Syria

An dakatar da kwashe fararen hula a Aleppo na kasar Syria

A yau juma'a an dakatar da kwashe fararen hula daga garin Aleppo,matakin da ya haifar da rudani a kokarin mayan kasashe dake fatar ganin an kwashe ilahirin  fararen fula daga garin.Majalisar Dinkin Duniya tace akalla fararen hula 50,000 dake neman ficewa daga birnin Aleppo yanzu haka ke makale a birnin, yayin da aka kwashe sama da 3,000 na masu bukatar barin gabashin birnin.Yau ake saran kwamitin Sulhu ya sake gudanar da wani taro na musamman kan rikicin. 

Ficewar fararen hula daga garin Aleppo
Ficewar fararen hula daga garin Aleppo REUTERS/Rodi Said
Talla

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman Steffan de Mistura yace cikin mutane kusan 50,000 da suka makale a gabashin Aleppo, 40,000 fararen hula ne dake neman tsira da rayyukan su, yayin da sauran kuma Yan Tawaye ne tare da iyalan su.

De Mistura yace bukatar su itace ganin an sanya jami’an Majalisar cikin wadanda aka kwashe domin kula da lafiyar su, a karkashin yarjejeniyar da aka kulla.
A karkahsin yarjejeniyar dai za’a kwashe fararen hular ne zuwa yankin Idlib.
Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Marc Ayrault ya bukaci kai Jami’an Majalisar Dinkin Duniya dan sa ido kan fararen hular.

Ministan ya bukaci tsagaita wuta a daukacin kasar ta Syria yayin da shugaba Bashar al Assad ke taya al’ummar Syria murnar samun nasara kan Yan Tawayen.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.