Isa ga babban shafi
Syria

Yarjejeniyar kwashe fararen hula daga yankunan 'yan tawaye a Syria

Rahotanni daga Syria sun ce motocin Safa sun fara shiga garuruwan da aka tsara fara kwashe fararen hula daga cikinsu, karkashin kulawar kungiyar Red Crescent da Red Cross, bayan cimma sabuwar yarjejeniyar hakan tsakanin gwamnati da ‘yan tawaye.

Motocin Safa zasu fara kwashe fararen hula daga yankunan 'yan tawaye a Syria
Motocin Safa zasu fara kwashe fararen hula daga yankunan 'yan tawaye a Syria REUTERS/Abdalrhman Ismail
Talla

Wata majiya a Syrian ta ce ana sa ran kwashe akalla mutane 4,000 daga garuruwan Fou’a da Kefraya dake yankin Idlib inda mayakan ‘yan tawaye suka yi musu kawanya.

Zalika za’a kwashe wasu fareren hular 1,500 daga garuruwan Madaya da Zabadani, sa’annan da dukkanin wadanda ke gabashin Aleppo cikin sabuwar matsayar da aka cinmma.

Cimma wannan yarjejeniya na zuwa bayan kwanaki da sanar da samun nasara kan ‘yan tawaye da gwamnatin Syria ta yi a Aleppo, wanda ya kasance karkashin ‘yan tawayen kasar tun a shekara ta 2012.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.