Isa ga babban shafi
Syria

Faransa za ta jagoranci taron Syria a Paris

Kasar Faransa ta ce kasashen da ke goyan bayan ‘Yan adawar Syria za su gudanar da wani taro a birnin Paris a farkon watan gobe a ci gaba da lalubo hanyar magance rikicin kasar da ya ki ci yaki cinyewa.

Shugaban Faransa, François Hollande
Shugaban Faransa, François Hollande REUTERS/Bertrand Guay
Talla

Faransa ta kuma bukaci daukar mataki kan Syria da kawayenta da ke amfani da makami mai guba kan fararen hula.

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Marc Ayrault ya bayyana shirin gudanar da taron inda ya ke cewa cikin kasashen da za su halarci taron har da kasar Amurka da wakilan kasashen da ke Yankin tekun Fasha.

Ministan ya ce ya dace kasashen duniya su daina kawar da kansu kan irin ta’addancin da ake aikatawa a Syria yanzu haka.

Ayrault ya ce ya zama dole su dauki mataki kan abinda ke faruwa yanzu haka na kashe fararen hula.

Yanzu haka dakarun da ke goyan bayan shugaba Bashar al Assad na ci gaba da kutsawa birnin Aleppo a kokarin karbe birnin daga mayakan ISIS.

Kasashen da za su halarci taron sun hada Amurka da Jamsu da Faransa da Italiya da Birtaniya. Sauran sun hada da Saudi Arabia da Qatar da Daular Larabawa da kuma Jordan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.