Isa ga babban shafi
Iran

An kashe Iraniyawa 1,000 a yakin Syria

Shugaban Tsoffin sojin kasar Iran, Muhammed Alu Shahidi Mahalati, ya ce jami’ansa sama da 1,000 aka kashe a yakin da ake yi a kasar Syria. ‘Yan kasar Iran da dama ne ke yaki don kare shugaba Bashar al Assad da ke fada da ‘Yan tawaye.

Iran na taimakawa dakarun Gwamnatin Syria yakar 'Yan tawaye da ke samun taimakon Amurka da kasashen Turai
Iran na taimakawa dakarun Gwamnatin Syria yakar 'Yan tawaye da ke samun taimakon Amurka da kasashen Turai REUTERS/Hamid Khatib
Talla

Mohammed Ali Shahidi Mahalati, shugaban tsoffin sojojin Iran ya bayyana adadin tsoffin sojojin ne ga manema labarai a Tehran, yayin da ya ke tsokaci kan yakin da ya ki ci ya ki cinyewa.

Kasar Iran ta tura tarin sojoji da kuma ma su bayar da shawara domin taimakawa shugaba Bashar al Assad wanda suka ce gwamnatocin duniya a karkashin Amurka na kokarin raba shi da mukamin sa.

Iran na cewa ta tura sojojin ne don yakar mabiya Sunnah masu tsatsauran ra’ayi, kuma daga cikin wadanda ake turawa har da ‘yan kasashen Afghanistan da Pakistan.

Kafofin yada labaran Iran kan yi bayani lokaci lokaci kan wadanda aka kashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.