Isa ga babban shafi
Syria

Syria ta ki amincewa da ikon ‘Yan tawaye a Aleppo

Gwamnatin Syria ta yi watsi da bukatar Majalisar Dinkin Duniya na amincewa da gwamnatin ‘Yan tawaye a gabacin Aleppo a karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu.

Ministan harakokin wajen Syria Walid al Muallem yana ganawa da Jekadan Majalisar Dinkin Duniya Stefan de Mistura
Ministan harakokin wajen Syria Walid al Muallem yana ganawa da Jekadan Majalisar Dinkin Duniya Stefan de Mistura REUTERS
Talla

Jekadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Syria Staffan de Mistura, ne ya gabatar da bukatar a wata ganawa da suka yi da ministan harakokin wajen kasar Walid Muallem a Damascus domin ganin an kawo karshen haren haren da ake ci gaba da kai wa a yankin na Aleppo.

Muallim ya yi watsi da bukatar inda ya ce ba za su yarda Majalisar Dinkin Duniya ta ba ‘Yan ta’adda wani yanki na Syria ba.

Tun Talatar makon jiya Syria ta kaddamar da sabbin hare hare ta sama akan ‘yan tawaye a Aleppo.

Rahotanni a yau Lahadi sun ce an kashe yara 8 a wani hari da ‘Yan tawaye suka kai a makaranta a garin na Aleppo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.