Isa ga babban shafi
Syria

A na ci gaba da ruwan wuta a birnin Aleppo

Jiragen Yakin Gwamnatin Syria da na Rasha na ci gaba da ruwan wuta kan birnin Aleppo, inda kayayyakin abincin agaji da ake bayar wa yake gab da karewa.

Gwamnatin Syria da na Rasha na ci gaba da ruwan wuta a birnin Aleppo
Gwamnatin Syria da na Rasha na ci gaba da ruwan wuta a birnin Aleppo AMEER ALHALBI / AFP
Talla

Rahotannin sun ce a cikin sa’o'i 24 an ruwaito cewar akalla mutane 35 aka kashe a birnin, matakin da ya harzuka Amurka da Majalisar Dinkin Duniya.

Kungiyar da ke sa ido kan rikicin kasar ta ce cikin wadanda aka kashe harda yara kanana guda 6.

Kungiyar likitoci masu zaman kan su ta ce cikin wuraren da aka kai hari harda wasu cibiyoyin kula da lafiya guda biyu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.