Isa ga babban shafi
Syria-Rasha

'Yan tawayen Syria sun kaddamar da hari kan yammacin Aleppo

‘Yan tawayen Syria sun kaddamar da hari kan yakunan birnin Aleppo da ke karkashin ikon sojojin gwamnati, a kokarinsu na wargaza kawanyar da aka yi musu tsawon makwanni.

Yankin birnin Aleppo da ke karkashin ikon 'yan tawaye
Yankin birnin Aleppo da ke karkashin ikon 'yan tawaye EUTERS/Abdalrhman Ismail/File Photo
Talla

Harin 'yan tawayen ya maida hankali kan yammacin Aleppo da tuni sojojin Syria tare da taimakon jiragen yakin Rasha suka kwace shi daga hannun 'yan tawayen.

Kungiyar kare hakkin dan’adam da ke sa ‘ido kan rikicin Syria, Syrian Observatory, ta ce harin mayakan ‘yan tawayen yayi sanadiyyar kashe fararen hula 5 tare da raunata wasu 100 a yammacin birnin.

Sai dai kuma wata majiya daga rundunar sojin Syria ta ce, ta samu nasarar wargaza shirin mayakan 'yan tawaye na kaddamar da hare-hare kan Kudanci da kuma Arewacin birnin Aleppo da ke karkashin gwamnatin Bashar al Assad.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.