Isa ga babban shafi
Faransa- Amurka

Hollande ya zanta da Trump ta wayar tarho

Shugaban Faransa, Francois Hollande ya bayyana cewa ya zanta da zababben shugaban Amurka, Donald Trump ta wayar tarho, in da suka tattauna kan batutuwa da dama bayan Trump ya yi wa yarjejeniyar dumamar yanayi barazana.

Shugaba Hollande na Faransa a lokacin ganawarsa da RFI da France 24 a birnin Marrakesh na Morocco
Shugaba Hollande na Faransa a lokacin ganawarsa da RFI da France 24 a birnin Marrakesh na Morocco
Talla

A hirar da ya yi da kafafen yada labarai na RFI da France 24 a taron sauyin yanayi a birnin Marrakesh na Morocco, shugaba Hollande ya ce, musababbin kiran Trump shi ne yunkurin samar da masalaha, lura da manufofin da Trump ya sanar a lokacin yakin neman zabensa.

Trump ya ce, zai yi watsi da yarjejeniyar da kasashen duniya 190 suka sanya wa hannu da nufin rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli.

Shugaba Hollande ya ce, wannan kudirin na Trump zai cutar da halittun da ke rayuwa akan dorar kasa, lura da cewa, Amurka na cikin kasashen da ke sahun gaba wajen fitar da hayaki mai gurbata muhalli.

Hollande ya ce, babu yadda za a iya warware yarjejeniyar ta Paris musamman idan aka kalle ta ta fannin shari’a.

Hollande ya kara da cewa, Mr. Trump ya nuna aniyar zama a tebubri don tattaunawa da Faransa, lura da dadaddiyar alaka da ke tsakanin kasashen biyu.

Sai dai Trump ya ki cewa komai a lokacin da Hollande ya yi masa tambaya kan sha’anin shugaban Rasha Vladmir Putin, wanda Trump ya jinjina wa a lokacin yakin neman zabe.

Kazalika, shugaba Hollande ya bayyana cewa, zai tsawaita dokar ta baci har zuwa lokacin da za a gudanar da zaben shugabancin kasar a cikin watan Mayu na shekara mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.