Isa ga babban shafi
Syria

Aleppo: Shugabbanin Turai za su dauki mataki akan Rasha

Ana sa ran Shugabannin kasashen Turai za su yanke shawara a taron da za su gudanar a Brussels game da daukar mataki mai tsauri akan Rasha da ke taimakawa gwamnatin Syria yakar ‘Yan tawaye.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da Putin na Rasha
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da Putin na Rasha REUTERS
Talla

Duk da sabanin ra’ayin shugabannin kasashen na Turai akan alakar da ke tsakanin Rasha da Syria, amma ana sa ran za su amince da daukar matakin karfafa wa gwamnatin Moscow takunkumi.

Wannan na zuwa ne bayan Rasha da Syria sun amince da dakatar da kai hare hare a yankin Aleppo domin samun isar da kayan jin-kai.

Shugabannin kasashen Tarayyar Turai za su tattauna akan huldarsu da Rasha a taron da za su gudanar a yau Alhamis.

A yau ne kuma Babban zauren Majalisar dinkin Duniya zai tafka mahawara kan halin da ake ciki a Aleppo na Syria, inda ake ci gaba da barin wuta da kuma hare haren sama.

Sakatare Janar mai barin gado, Ban Ki Moon zai yi jawabi ga Jakadun kasashe 193 tare da Jakadan Syria na musamman Staffan de Mistura bayan kwamitin Sulhu ya kasa warware rikicin kasar.

Kasashen duniya 70 suka kira taron na yau a karkashin kasar Canada, sai dai babu sanya hannun kasashen China da Rasha da kuma kasashe 4 da ke kwamitin Sulhu, Angola da Japan da Senegal da Venezuela.

Rasha da aminnanta sun dade suna hara kujerar na-ki ga duk wani mataki da kwamitin sulhu ke son dauka a game da rikicin Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.