Isa ga babban shafi
Faransa

Shugaba Putin ya soke ziyarar Faransa

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya soke ziyarar da ya shirya kai wa Faransa a cikin makon gobe bayan shugaba Francois Hollande ya yi allawadai da rawar da Moscow ke takawa a rikicin Syria.

Shugaba Hollande na Faransa da takwaransa na Rasha Vladmir Putin
Shugaba Hollande na Faransa da takwaransa na Rasha Vladmir Putin ALAIN JOCARD / AFP
Talla

Shugaba Hollande ne ya fara bayyana cewa, da yiwuwar ya soke ganawar da Putin saboda wannan rikici na Syria.

An dai shirya ganawar ce a tsakanin shugabannin biyu a ranar 19 ga watan Octoban da muke ciki amma Putin ya soke ta.

Hakan kuma na zuwa ne kwana guda da wani tsokaci da Hollande ya yi, in da ya ce, dakarun Syria sun aikata laifukan yaki a birnin Aleppo na Syria, bayan sun samu taimakon hare-haren jiragen saman Rasha.

Daya daga cikin daililan ziyarar Putin a Faransa, sun hada da kaddamar da Cocin Orthodox na Rasha da ke kusa da hasumiyar Eiffel a birnin Paris, sannan kuma ya tattauna da Hollande kan rikicin Syria da ke ci gaba da tsananata.

To sai magana da yawun fadar gwamnatin Rasha, Dimitry Peskov ya fadi cewa, shugaba Putin zai ci gaba da dakatar da kai ziyarar har sai lokacin da Hollande ya shirya tsaf don ganawa da shi.

Amma tuni Holande ya mayar da martani, in da ya ce, a shirye yake a kowani lokaci don tattanawa da Putin kan zaman lafiyar Syria.

Manyan kasashen biyu dai, sun samu gagarumin sabani da juna kan rikicn Syria kamar yadda Hollande ya bayyana a gabashin birnin Strasbourg.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.