Mamata Sakamakon Iska da Goguwa a Kasar Haiti Sun Haura 800
MDD ta yi gargadin cewa zai dauki lokaci kafin sanin takamaiman yawan mutanen da suka mutu sakamakon mummunar iska da ruwan sama mai karfi da ake kira Hurricane Mathew data ratsa kasar Haiti, da yazuwa yau Asabar ake fadin cewa mutane 800 suka mutu.
Wallafawa ranar:
Kungiyar samar da abinci ta duniya ta ce wasu wurare da yawa an gaza isa dole sai ta jiragen sama ko jiragen ruwa.
Yawancin hasarar rayukan a Haiti sun auku ne a gaban tekun kudu maso yammacin kasar.
Igiyar ruwan da goguwa yanzu haka ta tunkari gaban tekun jihar Florida na Amurka duk da cewa ta rage karfin ta sosai, inda wayewar gari Asabar aka gano mutane 4 suka mutu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu