Isa ga babban shafi
MDD

Al Hussein ya soki Donald Trump da Geert Wilders

Shugaban hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya Zeid Ra’ad Al Hussein ya yi mummunar suka kan dan takaran shugabancin Amurka Donald Trump da Geert Wilders, shugaban Jam’iyyar dake yaki da Musulmi a Holland.

Shugaban Hukumar kare Hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya Zeid Ra’ad Zeid Al-Hussein
Shugaban Hukumar kare Hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya Zeid Ra’ad Zeid Al-Hussein FABRICE COFFRINI / AFP
Talla

Al Hussein ya koka kan yadda manyan ‘yan siyasar biyu ke kalaman raba kan jama’a, inda yake cewa a matsayin sa na Musulmi dole ne ya kare hakkin kowanne Bil Adama.

Jami’in ya kuma soki masu ra’ayi irin na Trump da Wilders da suka hada da Firaministan Hungary Victor Orban da shugabar jam’iyyar Faransa da ke kyamar baki, Marine Le Pen da shugaban wadanda suka nemi Birtaniya ta fice daga Turai, wato Nigel Farage a matsayin masu hadari ga zaman lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.