Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta bude sansaninin 'yan gudun hijira

A tsakiyar watan gobe na Octoba ne hukumar birnin Paris na kasar Faransa za ta bude sansanin tsunar da  yan gudun hijira na farko don magance samun sansanonin ba kan gado da yan gudun hijirar ke kafawa. 

Shugaban Faransa Francois Hollande
Shugaban Faransa Francois Hollande REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Magajiyar  birnin Paris Anne Hidalgo ta bayyana cewar birnin Paris zai bude sansani a wani tsohon kamfani dake arewacin Paris, wanda zai karbi maza zalla kimanin  400 zuwa 600 kafin karshen shekara.

Bayaga na farko ta ce za'a bude wani sansanin na biyu mai daukan mutane 350 wanda zai karbi mata da yara  kafin karshen shekara a wani tsohon kamfani da ke kudancin Paris.

A tsawon kwanaki biyar zuwa goma 'yan gudun hijirar za su sami kulawa da lafiyarsu  kafin a mika su zuwa ga ma’aikatun da suka dace da su kula da su.

A cikin watanni 6 na farkon wannan shekara kimanin 'yan gudun hijira dubu 240 suka shiga tarayyar turai ba bisa ka’ida ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.